Kwallon kafa

Arsenal ta sha kashi a San siro

Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic da dan wasan  Arsenal Thierry Henry  lokacin da suka yi musayar Riga bayan kammala wasansu a gasar zakarun Turai a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic da dan wasan Arsenal Thierry Henry lokacin da suka yi musayar Riga bayan kammala wasansu a gasar zakarun Turai a ranar 15 ga watan Fabrairu. REUTERS/Stefano Rellandini

Arsenal tasha kashi hannun AC Milan a filin wasa na San Siro ci 4-0, Duk da cewa kungiyoyin biyu sun yi adon riga mai dauke da tambarin Fly Emirates. Kevin-Prince Boateng ne ya fara zira kwallo a ragar Arsenal, Robinho kuma ya zira kwallaye biyu sai Zlatan Ibrahimovic wanda ya zira kwallon karshe a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Talla

Wannan ne kuma karo na farko da Ac Milan ta samu galabar Arsenal a karawa Bakwai a wannan gasa ta zakarun Turai, kuma ana danganta wannan kashin da Arsenal tasha a matsayin rana mafi muni ga Arsene Wenger.

Nan da makwanni uku ne Arsenal zata karbi bakuncin AC Milan a filin wasa na Emirates sai dai akwai jan aiki ga ‘Yan wasan gunners.

Bayan dawowa hutun rabin lokaci ne aka sako Thierry Henry wanda ya buga wasan karshe da Arsenal amma babu wani abu da ya attaka a wasan.

A kasar Russia kuma Zenit Saint Petersburg ta doke Benfica ci 3- 2. Sai dai a wasa ta gaba da za’a gudanar a Portugal sai Zenit ta yi da gaske domin kwallaye biyu da Benfica ta zira a ragarta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.