Europa league

United da City sun lashe wasanninsu a Europa

Ashley Young, na  Manchester United lokacin ya ke murnan zira kwallo a ragar'Ajax Amsterdam
Ashley Young, na Manchester United lokacin ya ke murnan zira kwallo a ragar'Ajax Amsterdam REUTERS/Michael Kooren

Manchester City da Manchester United sun huce hushinsu daga ficewa gasar zakarun Turai, inda suka lashe wasanninsu a daren jiya a gasar Turai ta Europa League. Manchester City ta doke FC Porto ne mai rike da kofin gasar ci 2-1, FC Porto ce ta fara zira kwallo a ragar City kafin daga bisani City ta barke kwallon, ana gab da kammala wasan ne saura minti Shida Sergio Aguero ya zira kwallo ta biyu a ragar Porto.

Talla

Wannan ne dai karo na farko da aka samu galabar FC Porto a gidanta cikin wasanni takwas da take bugawa a gasar Turai, kuma wannan kwarin gwiwa ne ga City amma sai ta yi da gaske domin kare nasarar da ta samu a Estadio.

Sai dai da safiyar yau kafafen yada labaran Birtaniya sun ruwaito cewa Manchester City ta yi zargin an nuna wa ‘yan wasanta biyu Balotelli da Yaya Toure wariyar launin fata a wasan daren jiya da FC Porto.

A daya bangaren kuma dan wasan Manchester United Antonio Valencia zai kwashe tsawon wata daya yana jinya saboda raunin da ya ji a wasan daren jiya tsakanin Manchester United da Ajax.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.