Kwallon kafa

Arsenal da Chelsea basu sha da dadi ba, Barca da Real da Milan sun haska

Arsenal har yanzu tana fuskantar barazana domin ta sake shan kashi a gasar FA, Chelsea kuma sai ta sake fafatawa da Birmingham, A gasar Seria A, AC Milan ta dare Saman Tebur, A Spain har yanzu tazarar maki goma ne Real Madrid ta ba Barcelona bayan sun haska a karshen mako.

Dan wasan AC Milan dan kasar Ghana Sulley Muntari lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Cesena tare da Robinho da Maxi Lopez a filin wasa na Dino Manuzzi
Dan wasan AC Milan dan kasar Ghana Sulley Muntari lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Cesena tare da Robinho da Maxi Lopez a filin wasa na Dino Manuzzi REUTERS/ Giorgio Benvenuti
Talla

Faransa

A Faransa, Paris Saint-Germain ce saman Tabur duk da wasa tsakaninta da Montpellier an tashi ne ci 2-2. John Utaka na Najeriya ne ya nemi ba Montpellier nasara inda ya zira kwallo ta biyu kafin daga bisani PSG ta barke kwallon.
PSG ce ke jagorancin Tebur maki daya tsakaninta da Montpellier.

Ingila

A Ingila Sunderland ce ta yi waje da Arsenal ci 2-0 a gasar FA, bayan Arsenal tasha kashi hannun AC Milan ci 4-0 a gasar zakarun Turai.

Chelsea kuma har yanzu Andre Villas-Boas yana fuskantar Barazana bayan ya yi kunnen doki ci 1-1 da Birmingham, kuma hakan yasa sai sun sake fafatawa. Liverpool kuma zata kara ne da Stoke City a wasan Quarter Final bayan dukkaninsu sun lashe wasanninsu

Spain

A Spain Lionel Messi ya zira kwallaye hudu a raga wanda ya bai wa Barcelona nasarar lallasa Valencia ci 5-1, amma har yanzu tazarar maki 10 ne Real Madrid taba Barcelona bayan Real Madrid ta doke Racing Santander ci 4-0.

Cristiano Ronaldo ne dai ke da yawan kwallaye 28 a raga, amma Messi shi ke bi masa inda yanzu haka yake da kwallaye 27 a raga.

Italiya

A Seria A, AC Milan ta dare saman Tebur bayan ta doke Cesena ci 3-0. Dan kasar Ghana Sulley Muntari wanda ya fara haskawa a Milan ya zira kwallo a raga.

A karshen mako ne AC Milan zata fafata da Juventus a San Siro, amma a karshen makon nan Juve ta doke Catania ci 3-1.

Har yanzu dai Udinese ce a matsayi na uku duk da cewa wasa tsakaninta da Cagliari an tashi ne babu ci.

Jamus

A Bundesliga ta kasar Jamus Borussia Dortmund ta doke Hertha Berlin ci 1-0 wanda ya bata damar bude sabon babin jagorancin Tabur da maki uku inda kuma wasa tsakanin Bayern Munich da Freiburg aka tashi babu ci 0-0.

Bayern Munich yanzu tana matsayi na uku ne a Tebur maki hudu tsakaninta da Borussia Dortmund.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI