Kwallon kafa

Napoli 3 Chelsea 1, Inter zata fafata da Marseille

John Terry Jagoran 'Yan wasan Chelsea wanda zai kwashe makwanni yana jinayar Tiyata da za'a yi ma shi
John Terry Jagoran 'Yan wasan Chelsea wanda zai kwashe makwanni yana jinayar Tiyata da za'a yi ma shi chelseafc.com

A gasar zakarun Turai, Chelsea ta sha kashi hannun Napoli ci 3-1 a Italiya, bayan Real Madrid ta yi kunnen Doki ci 1-1 da CSKA Moscow a kasar Rasha. Inter Milan kuma zata fafata da Marseille.

Talla

Juan Mata ne ya fara zira wa Chelsea kwallonta a raga, amma Ezequiel Lavezzi ya barke kwallon tare da sake zira wata kwallon a raga, Cavani ne ya zira kwallo ta uku a ragar Chelsea.

Yanzu haka dai kungiyoyin Italiya, wato AC Milan da Napoli sun sa kafarsu daya a zagayen Quarter final, kungiyoyin Ingila kuma Arsenal da Chelsea, kafarsu daya akan hanyar ficewa gasar, wannan ne kuma ke nuna cewa wasa bata yi wa Ingila dadi ba tun bayan ficewar Manchester United da Manchester City tun a zagayen farko.

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas. da ke fuskantar matsin lamba ya amsa cewa basu tsare gidansu da kyau ba.

Jagoran Chelsea kuma John Terry, za’a yi masa tiyata a kafar shi kuma zai kwashe makwanni yana jinya.

A Rasha kuma Real Madrid ta yi kunnen doki da CSKA Moscow ci 1-1 sai dai Real Madrid din na iya tsallakewa saboda kwallon da ta zira a ragar CSKA Moscow amma ba ‘a san yadda wasa zata kaya ba gidan Real a ranar 14 ga watan Mayu.

A wasan dai Karim Benzema ya samu Rauni kafin zuwa hutun rabin lokaci, Cristiano Ronaldo ya zira kwallo a raga.

A yau kuma kungiyar Marseille a Faransa zata karbi bakuncin Inter Milan da ke neman kawo karshen wasanni 6 ana doke ta.

Akwai kuma wasa tsakanin Basel da Bayern Munich ta kasar Jamus.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.