Kwallon kafa

Inter Milan da Bayern Munich sun sha kashi

A gasar cin kofin zakarun Turai Inter Milan ta sha kashi hannun Olympic Marseille ci 1-0. Bayern Munich ma ta kasar Jamus ta sha kashi hannun kungiyar Basel ta kasar Switzerland, Sai  bayan kwashe mintina 86 ana fafatawa ne Basel ta zira kwallo a ragar Bayern Munich.

dan kasar Ghana André Ayew dake kwallo a  Marseille lokcin da yake murnar zira kwallo a ragar Inter Milan
dan kasar Ghana André Ayew dake kwallo a Marseille lokcin da yake murnar zira kwallo a ragar Inter Milan REUTERS/Eric Gaillard
Talla

A tarihin Gasar zakarun Turai, kungiyar Basel ta shiga kundin tarihin da ta doke Bayern da Manchester United wadanda dukkaninsu sun taba lashe kofin gasar.

Dan kasar Ghana ne Andre Ayew ya zira kwallo a ragar Inter Milan, inda yanzu haka kocin Inter, Claudio Ranieri ke fuskantar barazana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI