Kwallon Kafa

Marseille da Bayern sun tsallake Quarter Final a gasar Zakarun Turai

Dan kasar Brazil Brandao lokacin da yek murnar zira kwallo a ragar Inter Milan a gasar Zakarun Turai.
Dan kasar Brazil Brandao lokacin da yek murnar zira kwallo a ragar Inter Milan a gasar Zakarun Turai. REUTERS/Alessandro Garofalo

Kungiyar Marseille ta Faransa ta tsallake zuwa zagayen Quarter Final a gasar Zakarun Turai inda ta Haramtawa Inter Milan ta Italiya tsallakewa duk da cewa Inter ce ta lashe wasan jiya ci 2-1. Amma Marseille ta tsallake ne saboda kwallon da ta zira a ragar Inter a San siro.

Talla

Wannan ne dai karo na farko da Marseille ta samu damar tsallakewa zuwa zagayen Quarter Final tun bayan lashe kofin gasar a shekarar 1993.

A Filin wasa na Allianz Arena kuma a kasar Jamus da za’a buga wasan karshe a bana, Bayern Munich ta lallasa Basel ci 7-0. A karawar farko Basel ce ta doke Bayern Munich ci 1-0 amma Arjen Robben wanda ya zira kwallaye biyu yace sun kwantar da hanaklinsu ne domin lashe wasan.

A karshen mako dai Bayern ta lallasa Hoffenheim ci 7-1 a Bundesliga, kuma a wasan jiya tun kafin hutun rabin lokaci ne Bayern ta zira kwallaye uku. Mario Gomes ne ya zira kwallaye hudu a raga.

Kocin Inter Milan, Claudio Ranieri yace akwai rashin sa’a ga Inter Milan a bana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.