Kwallon kafa

Manchester United da City sun fice gasar Europa

Rooney da Balotelli bayan bayan shan kashi a gasar Europa
Rooney da Balotelli bayan bayan shan kashi a gasar Europa Getty image AP

Manchester United da Manchester City sun fice gasar Europa League ta Turai, bayan sun sha kashi a daren jiya. Manchester United ta sha kashi ne hannun Athletic Bilbao ci 2-1, Manchester City kuma tasha kashi ne hannun Sporting Lisbon a Portugal ci 2-0. wannan ne karo na farko da Athletic Bilbao ta tsallake zagayen quarter final a gasar Turai bayan kwashe shekru 35.

Talla

A Turai bana wasa bata yi United da City dadi ba domin sun fice manyan gasar a Nahiyar Turai, yanzu kuma hamayya zata dawo ne a Premier. Chelsea ce kungiya Tilo da ke wakiltar Ingila a gasar Turai bayan tsallakewa zagayen Qurtar Final a gasar zakarun Turai a ranar Laraba.

Kungiyoyin Spain uku ne suka tsallake zagayen Quarter Final a Europa, da suka hada da Athletic Bilbao da Atletico Madrid da Valencia, Sai kasar Jamus mai kungiyoyi biyu Schalke 04 da Hanover.

Akwai kungiyoyin AZ Alkmaar ta Holland sai kungiyar Metalist Kharkiv Ukraine da kuma Sporting Lisbon.

A yau Juma'a ne za'a hada wadanda zasu kara da juna a gasar Europa da Gasar Zakarun Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.