Zakarun Turai: Chelsea da Benfica, APOEL zata nemi ba Madrid mamaki
Wallafawa ranar:
A Gasar Zakarun Turai, Kungiyar APOEL ta kasar Cyprus zata fafata da Real Madrid inda wasu suke ganin Madrid ta samu garabasa a wasan Quarter Final amma dubban masoya APOEL ne suka saye tikitin shiga kallon wasan domin fatar ba Real Madrid mamaki.
A daya bangaren kuma Chelsea zata kara ne da Benfica, kuma Kocin Chelsea Roberto Di Matteo tsohon dan wasan Benfica ne, kuma akwai tsoffin ‘yan wasan Benfica a tawagar Chelsea wato Ramires da David Luiz wadanda suka taka kwallo a Benfica kafin zuwansu Chelsea.
A karshen mako, Chelsea bata sha dadi ba hannun Tottenham a Premier domin an tashi wasan babu ci.
Tsakanin Chelsea da Benfica cikin duk kungiyar da ta tsallake ita ce zata hadu da Barcelona ko AC Milan a wasan kusa da karshe.
A bana dai babu hamayya tsakanin Barcelona da Real Madrid domin ba zasu iya haduwa ba sai a wasan karshe da za’a gudanar a ranar 19 ga watan Mayu.
Wannan ne karo na farko da wata kungiya daga Cyprus ta tsallake zuwa zagayen Quarter final a gasar zakarun Turai.
A gobe Laraba ne dai AC Milan zata karbi bakuncin Barcelona a San Siro.
Bayern Munich kuma zata kai ziyara Faransa domin fafatawa da Marseille.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu