Kwallon kafa

Bayern da Marseille, Milan zata Kece raini da Barcelona

Kocin AC Milan Massimiliano Allegri tare da Zlatan Ibrahimovic  a lokacin da suke amsa tambayoyi da manema labarai game da karawarsu da Barcelona a San Siro
Kocin AC Milan Massimiliano Allegri tare da Zlatan Ibrahimovic a lokacin da suke amsa tambayoyi da manema labarai game da karawarsu da Barcelona a San Siro REUTERS/Alessandro Garofalo

A yau Laraba ne AC Milan zata karbi bakuncin Barcleona mai rike da kofin gasar Turai a filin wasa na San Siro. Kuma Kocin AC Milan yace akwai hanyoyi biyu da zasu yi amfani dasu domin karya lagon Barcelona duk da Milan na fuskantar matsalar jinyar rauni na wasu fitattun ‘yan wasanta.

Talla

Kocin Yace zasu yi kwance ne domin kare gidansu amma da zarar sun samu zasu mamayi Barcelona domin jefa kwallo a raga, kamar yadda suka yi a karawar zagayen Farko.

Sai dai Kocin ya amsa cewa wannan tsarin ma tsari ne mai wahala a samu galabar Barcelona.

A karshen mako dai AC Milan ta fuskanci barazana saboda jinyar rauni da ‘yan wasanta suka samu. Sai dai yanzu ana hasashen Robinho da Maxi Lopez da Ibrahimovic zasu haska a yau tare da El Sharawy.

Sai dai babban kalubalen da ke gaban AC Milan shi ne rauni da Thiago Silva yaji jarumin dan wasan dake tsare mata baya. Kuma yanzu ya zama dole AC Milan ta lalubu ‘Yan wasanta da zasu hana su Messi haskawa a ragarta.

A Faransa kuma yau Laraba za’a kwashi ‘yan kallo tsakanin Marseille da Bayern Munich ta kasar Jamus.

Bayern dai ta lashe wasanninta biyar da ta buga na bayan bayan nan amma Marseille ta buga wasanni tawaks ba tare da samun nasara ba. Don haka Marseille sai ta yi da gaske kafin ta doke Bayern Munich.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI