Kwallon kafa

Zakarun Turai: Madrid da Chelsea sun lashe wasanninsu

Dan wasan Chelsea Salomon Kalou tare da abokan wasan shi  Fernando Torres Juan Mata a lokacin da suke murnar zira kwallon da ya zira a ragar Benfica
Dan wasan Chelsea Salomon Kalou tare da abokan wasan shi Fernando Torres Juan Mata a lokacin da suke murnar zira kwallon da ya zira a ragar Benfica REUTERS/Hugo Correia

Real Madrid da Chelsea sun sa kafar dama zuwa wasan kusa da karshe a gasar zakarun Turai bayan lashe wasanninsu ta bakunta a wasan Quarter Final da aka gudanar a daren jiya Talata.

Talla

Real Madrid ta lallasa kungiyar APOEL ta Cyprus ne ci 3-0. Karim Benzema ne ya zira wa Madrid kwallayenta biyu a Raga, Kaka ne kuma ya zira kwallo daya.

Ga alamu a wasan kusan da karshe Madrid zata kara ne da Marseille ko Bayern Munich wadanda zasu fafata a yau Laraba, kodayake ba a san yadda wasa zata kaya ba a Benebour.

A kasar Portugal kuma Chelsea ta doke Benfica ci 1-0, kuma Solomon Kalou ne ya zira kwallon a ragar Benfica.

Kungiyar Chelsea ita ce kungiya daya Tilo da ta rage daga Ingila a gasar Zakarun Turai bayan ficewar Manchester United da Manchester City da Arsenal. Kuma yanzu ga alamu Chelsea zata tsallake zuwa zagayen kusa da karshe amma zata hadu ne da Barcelona ko AC Milan wadanda zasu kece raini a yau Laraba

To Sai dai kocin Chelsea Roberto Di Matteo yace har yanzu Chelsea tana da sauran aiki a gabanta domin komi na iya faruwa a Stamford Bridge idan har basu jajirce ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.