Kwallon kafa

Maki 8 tsakanin United da City, Maki 4 tsakanin Madrid da Barcelona

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ran shi bayan ya nemi zira kwallo a raga amma kwallo ta ki shiga ragar Valencia a filin wasa na Santiago Bernabeu
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ran shi bayan ya nemi zira kwallo a raga amma kwallo ta ki shiga ragar Valencia a filin wasa na Santiago Bernabeu REUTERS/Sergio Perez

Yanzu maki Takwas ne Manchester United taba Manchester city a Premier league a Ingila. A la liga a Spain tazarar maki Hudu ne yanzu tsakanin Real Madrid da Barcelona, A Italia Juventus ta dare saman Tebur na Seria A.

Talla

Ingila

A bana Manchester United tana neman lashe kofin Premier na Ashirin bayan doke QPR ci 2-0 wanda ya bata damar jagorancin Tebur da maki Takwas bayan Manchester City tasha kashi hannun Arsenal ci 1-0.

Yanzu kuma wasanni Shida ne kacal suka ragewa Manchester United a Premier ta sake mallakar Kofin gasar, bayan buga wasanni Takwas ba tare da samun galabarta ba.

 

Spain

A la liga a Spain, Real Madrid ta sake barar da maki biyu bayan an tashi wasa tsakaninta da Valencia babu ci a Bernabeu. Yanzu maki hudu ne Real Madrid ta ba Barcelona a La liga bayan Barcelona ta lallasa Real Zaragoza, wasan da Lionel Messi ya zira kwallo ta 60 a raga a bana.

Yanzu wasa bakwai ne ya rage a kammala La liga, kuma a ranar laraba ne Real Madrid zata kara da Atletico Madrid kafin ta kara da Sporting Gijon, daga nan kuma a yi fafatawar Clasico tsakanin Barcelona da Real Madrid a ranar 21 ko 22 ga watan Afrilu.

Faransa

A Faransa kuma PSG ta doke Marseille ci 2-1. kuma yanzu PSG tana jayayya ne tsakaninta Montpellier a saman Tebur, sai dai Montpellier zata iya ci gaba da jagorancin Tebur idan har ta doke Marseille a ranar Laraba .

Lille kuma tasha kashi hannun Brest ci 3-1 kuma yanzu maki Bakwai ne tsakanin Lille da Montpellier da ke jagorancin Tabur.

Jamus

A Bundesliga ta kasar Jamus Raul Gonzalez ne ya zirawa Schalke 04 kwallayenta biyu a ragar Hannover inda aka tashi wasan ci 3-0, kuma yanzu Schalke 04 ce a matsayi na uku a Tebur bayan Bayer Leverkusen ta yi kunnen doki da Hamburg ci 1-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.