Kwallon kafa

Chelsea ta doke Tottenham, Messi da Ronaldo sun yi bukin zira kwallaye 41 a La liga

a lokacin da dan wasan kungiyar  Livorno, Piermario Morosini ya fadi kasa a filin wasa. Kuma nan take ne Morosini ya mutu.
a lokacin da dan wasan kungiyar Livorno, Piermario Morosini ya fadi kasa a filin wasa. Kuma nan take ne Morosini ya mutu. REUTERS/Fabio Urbini

A karshen mako, a kasar Italia an yi zaman makokin mutuwar Morosini wanda ya mutu a filin wasa, a Ingila Chelsea ta tsallake zuwa buga wasan karshe a gasar FA bayan lallasa Tottenham. A La liga Messi da Cristiano. Ronaldo sun yi bukin zira kwallaye 41 a raga, a Faransa kuma Montpellier tasha kashi.

Talla

A ranar Assabar ne Piermario Morosini dan wasan kungiyar Livano a Seria B a Italia ya fadi filin wasa ya mutu sanadiyar bugun zuciya.

Labarin mutuwar dan wasan shi ne ya mamaye Daukacin jaridun kasar Italia a karshen mako.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta FIFA yace babu wasu kalaman da zasu bayyana mutuwar dan wasan, amma Mista Blatter yace mutuwar dan wasan a filin wasa al’amari ne mai daga hankali.

A makwanni biyu da suka gabata, an samu kwatankwacin haka a Ingila inda dan wasan Bolton, Fabrice Muamba ya fadi a fili saboda bugun zuciya amma dan wasan ya fara murmujewa yanzu haka.

Ingila

A ingila Chelsea ta lallasa Tottenham ci 5-1 wanda ya bata damar tsallakewa zuwa buga wsan karshe da Liverpool a gasar FA da za’a gudanar a filin wasa na Wembley.

Didier Drogba da Juan Mata da Ramires da Frank Lampard da Florent Malouda ne suka zirawa Chelsea kwallayenta a ragar Totteham.

Wannan nasarar da Chelsea ta samu wani kimtsi ne kafin ‘Yan Wasan The Blues su fafata da Barcelona a gasar Zakarun Turai a ranar Laraba.

A Premeri league har yanzu maki biyar ne tsakanin United da Manchester City.
Sai da Carlos Tevez ya zirara kwallaye uku a raga wanda ya bai wa Manchester City nasarar doke Norwich ci 6-1. Kafin United ta doke Aston Villa ci 4-0.

A yau Litinin ne Arsenal zata kace raini da Wigan kungiyar da ta doke Manchester United ci daya mai ban haushi a makon jiya.

Spain

A la liga a Spain, Cristiano Ronaldo da Messi a karshe mako sun yi bukin zira kwallaye 41 a raga bayan kungiyoyinsu Real Madrid da Barcelona sun lashe wasanninsu.

A ranar Assabar Real Madrid ta lallasa Sporting Gijon ci 3-1, daga bisani ne kuma Barcelona ta doke Lavente ci 2-1 wasan da Messi ya zira kwallo ta 63 a raga bana.

Har yanzu maki hudu ne tsakaninsu a Tebur na La liga kafin kungiyoyin biyu su kece raini da juna a ranar Assabar.

Jamus

A Bundesliga ta kasar Jamus Borussia Dortmund ta doke Schalke 04 ci 2-1, amma wasa tsakanin Bayern Munik da Mainz an tashi ne babu ci 0-0. hakan ne ya kara yawan makin da Dortmund taba Bayarn Munich a Tebur.

Yanzu haka dai Dortmund tana neman nasarar lashe wasa daya ne kacal ta lashe kofin Bundesliga a bana.

Faransa

A Faransa Montpellier mai jagorancin Tebur na French Leage ta sha kashi hannun Loreint ci 2-1.

Sai dai Paris Saint-Germain ta kasa amfani da wannan damar domin rage yawan makin da ke tsakaninta da Montpellier bayan ta yi kunnen doki ci 1-1 tsakaninta da Auxerre.

Yanzu maki biyu ne Montpellier taba Paris Saint-Germain a Tebur inda sauran wasanni Shida suka rage a kammala League.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.