Zakarun Turai

Zakarun Turai: Bayern Munich da Chelsea zasu buga wasan karshe

Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ran shi bayan ya barar da bugun daka kai sai mai tsaron gida
Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya nuna bacin ran shi bayan ya barar da bugun daka kai sai mai tsaron gida REUTERS/Sergio Perez

Real Madrid ta bi sahun Barcelona hanyar ficewa gasar zakarun Turai bayan ta yi barin kwallaye a bugun daga kai sai mai tsaron gida tsakaninta da Bayern Munich. Yanzu Bayern Munich da Chelsea zasu buga wasan karshe a Allianz Arena a kasar Jamus.

Talla

Bayern Munich ta tsallake ne bayan ta doke Real Madrid ci 3-1 bayan kammala mintinan wasa ana ci 3-3.

An kammala minti a cas’in ne ana ci 2-1, Real ta zira kwallaye biyu amma Bayern Munich tana da kwallo daya. kuma ci 2-1 ne aka yi a karawar farko a gidan Munich. Hakan ne kuma yasa dole sai an je bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Cristiono Ronaldo ne ya zirawa Madrid kwallayenta biyu amma kuma shi ya fara barar da kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida, da shi da Kaka da Sergio Ramos wanda ya dirka kwallon a sama.

Mutane da dama sun ta yi hasashen Barcelona da Real Madrid zasu buga wasan karshe amma kuma yanzu kwallo ta bada ba haka ba,

Bayern Munich yanzu zata kara ne da Chelsea, kuma a gidan Bayern Munich ne za’a buga wasan karshe a ranar 19 ga watan Mayu.

Dole sai Chelsea ta yi da gaske domin Bayern Munich zata samu rinjayen magoya baya a filin wasa.

Kodayake Chelsea na iya samun nasarar da Barcelona ta samu a bara inda ta doke Manchester United a Wembley kodayake ba a Old Trafford ba ne aka buga wasan amma a Ingila ne.

Amma akwai babban kalubale gaban Chelsea domin akwai ‘yan wasanta guda hudu da aka haramta wa buga wasan karshe a wasansu da Barcelona.

John Terry ba zai buga ba da Ramires da Ivanovic da Meireles.

Kodayake Bayern Munich akwai ‘yan wasanta guda biyu, Luiz Gustavo da Lahm da ba zasu buga wasan karshe ba.

Fatan Mourinho dai na haduwa da tsohuwar kungiyar shi Chelsea ya cutura.

Yanzu kungiyoyin Spain Barcelona da Real Madrid sai hakuri sai dai a haki badi. Tsakanin Chelsea da Bayern Munich yanzu za’a fitar da gwani.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.