Europa league

Athletic Bilbao da Atletico Madrid zasu buga wasan karshe a Europa League

'Yan wasan Bilbao a lokacin da suke murnan lashe wasan tsallakewa zuwa buga wasan karshe a Europa League
'Yan wasan Bilbao a lokacin da suke murnan lashe wasan tsallakewa zuwa buga wasan karshe a Europa League REUTERS/Felix Ordonez

Athletic Bilbao da Atletico Madrid sun tsallake zuwa buga wasa karshe a gasar Europa League bayan samun nasarar wasanninsu a zagayen kusa da karshe. Wannan ya biyu bayan Ficewar Barcelona da Real Madrid a zagayen kusa da karshe a gasar Zakarun Turai.

Talla

Saura mintina biyu a kammala wasa, Fernando Llorente ya jefa kwallo a raga wanda ya ba Bilbao nasarar doke Sporting Lisbon ci 3-1, amma jimillar kwallaye ci 4-3 bayan kammala karawar farko Sporting nada 2-1.

A daya bangaren kuma ana minti 60 ne Adrain Lopez ya zirawa Atletico Madrid kwallo a ragar Valencia kuma haka aka tashi wasan ci 1 mai ban haushi. Amma Atletico Madrid ta samu jimillar kwallaye 5-2 bayan kammala karawar farko ci 4-2.

Wannan ne dai karo na biyu da kungiyoyin Spain zasu buga wasan karshe a Europa League.

A ranar 9 ga watan Mayu ne za’a buga wasan karshe a Bucharest, babbar birnin kasar Romania.

A ranar talata da Laraba ne dai Chelsea da Bayern Munich suka haramtawa kungiyoyin Spain Barcelona da Real Madrid buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai. Amma kuma Bilbao da Atletico Madrid sun tabbatar da lalle sai kungiyoyin Spain sun lashe daya daga cikin manyan kofunan Turai.

Bilbao dai na iya lashe kofi biyu a bana domin a ranar 25 ga watan Mayu ne zata fafata da Barcelona a wasan karshe na Copa Del Ray. Bayan ta kara da Atletico Madrid a Europa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.