Kwallon kafa

Manchester City da United, A tsakiyar Mako Madrid zata lashe La liga

Roberto Mancini na Manchester  City da  Alex Ferguson na Manchester United
Roberto Mancini na Manchester City da Alex Ferguson na Manchester United Getty image

A karon farko Fernando Torres ya zira wa Chelsea kwallaye uku a raga, a yau litinin ne za’a fitar da gwani tsakanin Manchester United da City. A la liga sai a tsakiyar mako ne Real Madrid zata lashe kofin gasar a bana, A Portugal, FC Forto ta lashe kofin league din kasar.

Talla

Ingila

A yau ne masu hamayyar Tebur a ingila Manchester United da Manchester City zasu kece raini da juna, inda wasan yau zai tantance wanda zai lashe kofin Premier tsakanin kungiyoyin biyu.

Sir Alex Frguson yace Manchester City zata iya lashe kofin a bana idan har ta samu galabar United a yau. Amma yace idan suka lallasa City ko suka yi kunnen doki to babu tantama kofin Premier na shi ne.

Maki uku ne dai Manchester United taba City a Tebur, amma City na iya darewa Tebur da yawan kwallaye idan har ta doke United.

A karshen mako Chelsea ta lallasa QPR ci 6-1 inda Fernando Torres ya zira kwallaye uku a karon farko tun zuwan shi Stamford Bridge daga anfield.

Sai dai Arsenal ta yi kunnen doki ne da Stoke City ci 1-1.

Rehotanni daga Ingila na cewa hukumar FA ta tuntubi Roy Hodgson kocin West Bromwich Albion don tattauna aikin horar da ‘yan wasan Ingila bayan ficewar Fabio Capello.

Spain

A Spain, a tsakiyar mako ne ranar Laraba Real Madrid zata lashe kofin La liga karo na farko bayan kwashe shekaru hudu kofin yana hannun Barcelona.

A karshen mako  Real Madrid ta doke Sevilla ci 3-0, Barcelona kuma ta lallasa Rayo Vallecano ci 7-0, kuma nasarar da Barcelona ta samu shi ya hana Real Madrid lashe gasar a karshen mako.

Idan dai Real Madrid  ta doke Athletic Bilbao a ranar Laraba, shi ne zai ba Mourinho kofin La liga na farko tun fara aikin shi a Madrid a shekarar 2008.

Cristiano Ronaldo da Messi yanzu suke hamayyar jagorancin zira kwallaye 43 a raga a bana, saura wasanni biyu a kammala La liga amma ba’a san cikinsu wanda zai karbi kyautar wanda ya fi zira kwallaye a raga ba.

Italiya

A kasar Itaila, Juventus tana kan hanyar lashe kofin Seria A a karon farko bayan kwashe kakar wasa 9 ba tare da jin kamshin kofin ba.

A karshen mako, Juve ta lallasa Novara ci 4-0, kuma maki uku  ne ke tsakaninta da AC Milan wacce ta doke Siena ci 4-1 a karshen mako.

Jamus
A Bundesliga ta kasar Jamus, Borussia Dortmund da ta lashe kofin gasar, ta sake lallasa Kaiserslautern da zata fice gasar a bana ci 5-2.

A wasan Bayern Munich na farko bayan ta fitar da Real Madrid a gasar zakarun Turai, Bayern ta doke Stuttgart ci 2-0.

Faransa

A Faransa kuma Paris Saint Germain ta sha kashi hannun Lille ci 2-1, kuma yanzu maki biyar ne tsakanin PSG da Montpellier da ke jagorancin Tebur bayan Montpellier ta samu nasarar doke Toulouse ci 1-0.

Wasanni hudu ne suka rage a kammala French league a bana kuma ga alamu Carlo Ancelotti, Montpellier zata haramta ma shi lashe kofin.

Portugal

A kasar Portugal kuma FC Porto ta lashe kofin League din kasar karo na 26 bayan ta doke Maritimo funchal ci 2-0, kuma wasa tsakanin Benfica da ke hammaya da Porto aka ta shi ci 2-2 da Rio Ave.

FC Porto ta lashe kofin ne da tazarar maki 6 tsakaninta da Benfica, ana sauran wasanni biyu a kamala gasar league din kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.