Kwallon Kafa

Roy Hodgson ne sabon kocin Ingila

Kocin West Bromwich Albion Roy Hodgson
Kocin West Bromwich Albion Roy Hodgson Reuters

Hukumar FA a Ingila ta nada Roy Hodgson matsayin kocin Ingila, kuma Hodgson yace bai yi mamakin kiran da hukumar FA ta yi mashi ba game da horar da ‘yan wasan Ingila domin an ta yin hasashen Harry RedKnapp ne zai gaji Fabio Capello.  

Talla

Hodgson yace zai iya lashe kofin Turai duk da adawa da Ingilawa ke yi game da zabensa.

Hukumar FA tace ta zabi Hodgson saboda kwarewarsa domin ya horar da ‘yan wasa a kasashe da dama da suka hada da Inter Milan a Italiya da Switzerland da wasu kungiyoyi a Ingila da suka hada da Liverpool da West brom.

Sai dai wasu ‘yan wasan Ingila irinsu Wayne Rooney da Rio Ferdinand da Jack Wilshere tuni suka nemi a zabi Harry Redknapp a watan Fabrairu, don haka yanzu babban kalubalen ne ga Hdgoson domin hada kan ‘yan wasan shi.

Hodgson zai fara jagorantar tawagar ingila a wasan sada zumunci tsakanin Ingila da Norway nan da makwanni uku kafin zuwa gasar cin kofin Turai a kasashen Ukraine da Poland.

Tun ficewar Fabio Capello, Hodgson shi ne kocin da hukumar FA ta tuntuba game da aikin horar da ‘yan wasan Ingila. Kuma yanzu ya kulla yarjejeniyar shekaru Hudu domin da hukumar FA

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.