Premier

Manchester City ta dare Tebur na Premier

Sir Alex Ferguson na Manchester a lokacin da yake tayar da jijiyar wuya tsakanin shi da Roberto Mancini na Manchester City bayan kompany ya jefa kwallon a ragar United.
Sir Alex Ferguson na Manchester a lokacin da yake tayar da jijiyar wuya tsakanin shi da Roberto Mancini na Manchester City bayan kompany ya jefa kwallon a ragar United. REUTERS/Nigel Roddis

Manchester City ta dare Tebur na Premier bayan ta samu galabar Manchester United ci 1-0 ana saura wasanni biyu a kammala gasar. Vincent Kompany ne ya ya jefawa City kwallonta a ragar Manchester United.

Talla

Wasan daren jiya tsakanin United da City shi ne wasa mafi girma da kungiyoyin biyu suka buga a tarihinsu, inda kowannensu na iya lashe kofin Premier a bana.

Kafin buga wasan dai Manchester United taba Manchester City maki uku a Tebur, amma yanzu City ta karbe ragamar jagorancin Tebur da yawan kwallaye 8 tsakaninta da United.

Manchester United ta barar da maki 8 cikin mako uku.

Akwai dai babban kalubale a gaban City domin zata kara da Newcastle United da ke a matsayi na Biyar a Tebur, daga bisani kuma ta fafata da QPR da ake wa barazanar ficewa Premier.

Manchester United kuma zata kara ne da Swansea daga nan kuma ta fafata da Sunderland.

A bana Manchester City ta doke Manchester United gida da waje.

A wasan jiya sai da Farguson da Mancini suka tada jijiyoyin wuya har sai da aka raba su. Bayan City ta zira kwallonta a ragar United.

Farguson dai ya zargi Mancini yana zagin alkalan wasa. Kuma Tuni Farguson yace yanzu kofin Premier yana hannun City idan rabonsu ne.

A karon farko City zata iya lashe kofin Premier bayan kwashe shekaru 44 ba tare da jin kamshin kofin ba, amma sai ta doke Newcastle United da QPR.

Sai dai QPR na iya haramtawa City kofin saboda kokarin da zasu yi na ganin lalle basu fice Premeir ba. idan kuma United ta lashe wasanninta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.