Kwallon Kafa

Messi ya karya Tarihin Mueller bayan zira kwallaye 68 a raga a bana

Lionel Messi, dan wasan Barcelona, a lokacin da yake murnar zira kwallo a raga
Lionel Messi, dan wasan Barcelona, a lokacin da yake murnar zira kwallo a raga REUTERS/Albert Gea

Lionel Messi ya karya tarihin dan wasan Bayern Munich Gerhard Mueller bayan zira kwallaye 68 a raga a bana. A jiya talata Barcelona ta lallasa Malaga ci 4-1 kuma Messi ne ya zira kwallaye uku a raga.

Talla

Gerhard Mueller ya kafa tarihin zira kwallaye 67 dan a Bayern Munich kakar wasan shekarar 1972, amma yanzu Messi ya sha gaban shi da kwallo daya a raga.

A bana Messi ya bugawa Barcelona wasanninta 57 amma ya zira kwallaye 46 a La liga, tare da zira kwallaye 14 a gasar Zakarun Turai sai kwallaye uku da ya zira a gasar Spanish Super Cup da kwallaye biyu gasar kungiyoyin duniya da gasar Copa Del Ray da gasar lashe kofin babban kofin Turai na Super Cup.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.