Premier

Newcastle ta samu galabar Chelsea a Stamford Bridge

Papiss Cisse dan wasan kungiyar Newcastle United a lokacin da yek murnar zira kwallo a ragar Chelsea
Papiss Cisse dan wasan kungiyar Newcastle United a lokacin da yek murnar zira kwallo a ragar Chelsea Reuters

A gasar Premier a Ingila Chelsea tasha kashi hannun Newcastle United ci 2-0, kuma kashin da Chelsea ta sha, damuwa ne a yunkurinta na samun hurumin shiga gasar zakarun Turai a badi.

Talla

Demba Cisse dan wasan Newcastle shi ne ya zira kwallaye biyu a ragar Chelsea a Stamford Bridge.

Yanzu maki hudu ne tsakanin Chelsea da Tottenham kungiyar da ta doke Bolton ci 4-1, sai dai Tottenham tana hamayya ne da Newcastle da tseren maki saura wasanni biyu a kammala Premier.

Chelsea na iya shiga gasar zakarun Turai a badi idan ta doke Bayern Munich a wasan karshe da za’a gudanar a bana, domin zata karbe hurumin shiga gasar daga hannun wanda ya zo na hudu a Tebur na Premeir.

A wasan Bolton, Fabrice muamba ya kai ziyara ta farko filin wasan Rebook bayan ya fadi a filin wasa saboda bugun zuciya.

Roberto Mancini yace kashin da Chelsea tasha hannun Newcastle barazana ce ga Manchester City da ke neman karbe kofin Premier hannun Manchester United a bana.

A karshen mako ne dai Mancini zai kai ziyara gidan Newcastle tare da fatan samu nasara akanta kafin daga bisani ya nemi wata nasarar hannun QPR sannan ya lashe kofin Premier.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.