La liga

Real Madrid ta lashe kofin La liga na 32

Kocin Real Madrid Jose Mourinho lokacin da 'Yan wasan shi ke daga shi sama bayan kammala wasa tsakanin Real da Bilbao da aka tashi ci 3-0
Kocin Real Madrid Jose Mourinho lokacin da 'Yan wasan shi ke daga shi sama bayan kammala wasa tsakanin Real da Bilbao da aka tashi ci 3-0 Reuters

Real Madrid ta lashe kofin La liga na 32 bayan ta lallasa Athletic Bilbao ci 3-0. Wannan ne kuma ya kawo karshen zamanin Barcelona wacce ta haramtawa Real Madrid kofin shekaru uku da suka gabata.

Talla

Gonzalo Higuain da Mesut Ozil da Cristiano Ronaldo ne suka zira wa Real Madrid kwallayenta a ragar Athletic Bilbao.

Hakan ne kuma yaba mourinho nasarar lashe kofi hudu a kasashe hudu daban daban. Amma Wannan ne kofin La liga na farko da Mourinho ya lashe a Real Madrid.
A jiya dai Dole sai Real Madrid ta doke Bilbao kafin ya lashe kofin domin Barcelona ta lallasa Malaga ci 4-1.

Bayan kammala wasan dai Mourinho ya kauracewa manema labarai, amma ‘Yan wasan shi Iker Casillas da Sergio Ramos dukkaninsu sun bayyana farin cikinsu

Yanzu haka buki ya barke a Madrid tsakanin magoya bayan kungiyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.