Kwallon Kafa

Mourinho yace gurin shi ya cika bayan lashe La liga da Seria A da Premier

José Mourinho,Kocin  Real Madrid, a lokacin da yake ganawa da manema labarai
José Mourinho,Kocin Real Madrid, a lokacin da yake ganawa da manema labarai Reuters

Mourinho yace baya da wani sauran gurin aikin horar da wata kungiya a wata kasa bayan ya lashe manyan kofunan gasar kasashen Turai. Mourinho ya lashe kofin Premier da Chelsea, sannan ya lashe kofin Seria A da inter Milan sannan kuma yanzu ya lashe kofin La liga da Real Madrid bayan duk ya lashe kofin kasarsa Potugal da FC Porto.

Talla

A tsakiyar mako ne dai Real Madrid ta lashe kofin La liga bayan ta lallasa Athletic Bilbao ci 3-0. Inda aka kammala gasar Madrid taba Barcelona tazarar maki 7.

Mourinho dai yanzu ya shiga sahun koca kocai uku a Turai da suka lashe kofin gasa a kasashe hudu wato Giovanni Trapattoni na Itali , da Happel na Austria sai kuma dan kasar Croatia Tomislav Ivic.

A gobe Assabar ne Real Madrid zata kai ziyara Granada cike da murnar lashe kofin La liga na 32, Barcelona kuma zasu buga wasan karshe da Espanyol tare da yin bankwana da kocinsu Pep Guardiola
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.