Premier

Rooney ya lashe kyautar wanda ya zira kwallon da ta fi Shahara a Premier

Wayne Rooney Dan wasan  Manchester United
Wayne Rooney Dan wasan Manchester United Reuters

Wayne Rooney Dan wasan Manchester United shi ne ya lashe kyautar wanda ya zira kwallon da ta tafi shahara a raga a Premeir League. Rooney ya lashe kyautar ne sanadiyar wata kwallo da ya zira a ragar Manchester City da akro.

Talla

Daruruwan masoya kwallon kafa ne suka kada kuri’ar da aka nema don bukin kakar wasa 20 ta Premier league.

Rooney dai ya samu rinjayen kuri’u kashi 26, sai Dennis Bergkamp tsohon dan wasan Arsenal da ya zo na biyu a wata kwallon da ya zira a ragar Newcastle, sai kwallon Thierry e Henry da ya zira a ragar Manchester United a shekarar 2000 a matsayi na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.