Premier

Blackburn Rovers ta fice Premier

Dan wasan Nigéria Yakubu Aiyegbeni a wasa Manchester United da Blackburn.
Dan wasan Nigéria Yakubu Aiyegbeni a wasa Manchester United da Blackburn. REUTERS/Phil Noble

Kungiyar Blackburn Rovers ta fice gasar Premier league bayan tasha kashi hannun Wigan Athletic ci 1-0. Blackburn ta kwashe shekaru 11 ana fafatawa da ita a Premier, amma Wigan ta sha da kyar ne domin fuekantar barazanar ficewa gasar.

Talla

A bana dai Wigan ta lallasa manyan kungiyoyin kwallon kafar Premier Manchester United da Arsenal da Liverpool da kuma Newcastle United.

A karshen mako dai dole sai an samu wata kungiya da zata yi wa Blackburn rakiya, tsakanin Bolton da QPR da Aston Villa.

Dole dai sai Bolton ta samu nasara akan Stoke City, idan QPR kuma ta yi kunnen doki da Manchester City sannan ta samu zama a Premier.

Idan kuma QPR ta sha kashi, Bolton kuma ta lallasa Stoke, to QPR ce zata yi bankwana da Premier.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.