Wasanni

Kasashe na ci gaba da shirin kauracewa wasannin Euro 2012 a Ukurain

Logo de l'Euro 2012 de football.
Logo de l'Euro 2012 de football. DR

A yau lahadi kasar Ukraine tace ta dakatar da taron da ta shiya na kasashen Turai, da a daa ta tsirya karbar bakuncin shi, a ranar juma’a mai zuwa, a shirye shirye fara wasannin cin kofin kwallon kafa na nahiyar turai, yayin da ake saura wata daya kafin fara wasan.Shirin Ukrain na karbar bakuncin wasu daga cikin wasanni da za a yi wannan gasar ya fara shiga garari ne, tun bayan da wasu kasashen nahiyar ta Turai suka fara bayyana shirin su na kauracewa wssannin da za a yi a can saboda yadda ake gallaza wa shugabar ‘yan adawan kasar da ke tsare, Yulia Tymoshenko.