Kwallon kafa

Montpellier na gab da lashe kofin League na Faransa

'Yan wasan Montpellier
'Yan wasan Montpellier Reuters

Kungiyar Montpellier na gab da lashe kofin league din kasar Faransa bayan ta lallasa kungiyar Rennes ci 2-0, domin yanzu maki uku ne tsakaninta da PSG, saura kuma wasanni biyu a karkare gasar.

Talla

Kafin jiya litinin dai PSG ke jagorancin tebur da yawan kwallaye bayan ta doke Valenciennes ci 4-3 a ranar Lahadi.

Montpellier dai sai ta yi da gaske domin a karshen mako zata kara da Lille mai rike da kofin.

Domin a bana ma Kungiyar Lille zata iya lashe gasar don maki biyu ne kacal tsakaninta da PSG da ke matsayi na biyu a Tebur.

A bana dai kungiyar Auxerre zata fice league na daya a faransa wata kila da Dijon dake bi mata a kasan Tebur da kuma kungiyar Brest.

A karshen kakar wasa kuma PSG da Chelsea zasu kai ziyara kasar Amurka domin buga wasan sada zumunci a filin wasa na Yankee a birnin New York.

Za’a gudanar da wasan ne a ranar 28 ga watan Yuli bayan kammala gasar cin kofin Turai, kuma Wasan sada zumun zai hada Carlos Ancelotti da mataimakin shi Makelele da tohuwar kungiyarsu Chelsea.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.