Wasanni

Za a sayar da karin tikitin wasannin Olympics na birnin London

Alamar wasannin Olympics na birnin London
Alamar wasannin Olympics na birnin London

A ranar juma’a mai zuwa ake sa ran fara sayar da Karin tikitin wasanni Olympics na birnin London har kusan miliyon 1. Za dai a sayar da wadannan tikitin ne ga mutanen da a baya suka nema, amma basu samu sun saya ba har suka kare.A yau talata, Hukumar shirya wasannin na Olympics, da ake kira LOCOG ta ce tikitin da za a sayar sun hada da guda 47,000 don kallon wasannin da aka fi sha’awa, da 5,000 don kallon wasannin farko da 6,000 don wasannin karshe a gasar.Akwai guda 55,000 don wasannin kwallon kafa, da 74,000 don kallon wasan volleyball.Masu shiya wasannin sun ce za a sayar da Karin tikiti 70,000 don masu son kallon wasannin ta irin manyan allunan nan a wani wurin shakatawan da aka shirya musamman don haka.