Boxing

Chisora da Haye zasu yi Damben kece raini

Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus
Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus REUTERS/Action Images/Andrew Couldridge

A Birtaniya an tabbatar da Damben kece raini tsakanin Dereck Chisora da David Haye wanda za’a gudanar a watan Yuli saboda huce hushin juna.

Talla

A kwanan baya ne ‘Yan Damben guda biyu suka abka wa juna a wani Damben bayan fage bayan Chisora ya sha kashi hannun Vitali Klitschko, don haka ne yanzu zasu kece raini da juna.

David Haye dai ya yi amai ya lashe domin a bara ne ya bayyana yin Ritaya daga Damben na Boxing.

Ana dai ganin Damben Boxing tsakanin Chisora da Haye shi ne Dambe mafi girma da za’a gudanar a Birtaniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.