Europa league

Europa League: Atletico Madrid zata fafata da Athletic Bilbao a wasan karshe

Filin wasan da za'a buga wasa tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao a Bucharest kasar Romania
Filin wasan da za'a buga wasa tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao a Bucharest kasar Romania RFI Romana

A yau Laraba ne kungiyoyin Spain guda biyu Atletico Madrid da Athletic Bilbao zasu buga wasan karshe a gasar Turai ta Europa League a birnin Bucharest na kasar Romania. Atletico zata yi kokarin maimata tarihin nasarar da ta samu a shekarar 2010 inda ta doke Fulham ci 2-1 a wasan karshe.

Talla

Cikin shekaru uku da kama aikin horar da ‘yan wasan Atletico Madrid, wannan ne karo na biyu Diego Simeone ya kai kungiyar Atletico buga wasan karshe a Europa League.

Sai dai a yau Mista Simeone ya gargadi ‘yan wasan shi domin yin taka tsan tsan da Athletic Bilbao .

A bana dai an ta yin hasashen Real Madrid da Barcelona zasu iya buga wasan karshe a gasar zakarun Turai, amma sai gashi dukkaninsu sun fice a wasannin kusa da karshe.

Sai dai Atletico Madrid da Bilbao sune suka maye gurbin kungiyoyin a babbar gasar Turai bayan tsallakewa zuwa buga wasan karshe.

Athletic Bilbao ce dai ta yi waje da Manchester United a gasar tun a zagayen farko bayan United ta fice gasar zakarun Turai, sannan kuma ta sake yin waje da Schalke 04 a zagayen Quarter Final, a zagayen kusa da karshe kuma ta lallasa Sporting Lisbon, don haka dole sai Atletico Madrid ta yi da gaske duk da cewa Atletico Madrid ce a matsayi na hudu saman Bilbao a Teburin La liga.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.