Premier

Liverpool ta rama kashin da ta sha hannun Chelsea

'Yan wasan kungiyar Liverpool a Ingila
'Yan wasan kungiyar Liverpool a Ingila

Kungiyar Liverpool ta rama kashin da ta sha hannun Chelsea a gasar FA domin a daren jiya Liverpool ta lallasa Chelsea ci 4-1 a Premier league. Yanzu kuma ya zama dole sai Chelsea ta lashe kofin gasar zakarun Turai a wasa tsakaninta da Munich kafin ta sake samun hurumin shiga gasar a badi.

Talla

Kwanaki hudu ne da suka gabata Chelsea ta lashe kofin FA bayan ta doke Liverpool ci 2-1 a Wembley, amma a daren jiya cikin mintina talatin da fara wasa kwallaye uku suka fada a ragar Chelsea bayan Michael Essien ya yi kuskuren zira kwallon farko sai kuma kwallayen da ‘yan wasan Liverpool suka zira Jordan Henderson da Daniel Agger.

Ana dawowa hutun rabin lokaci ne Ramires ya zira wa Chelsea kwallo daya a ragar Liverpool kafin kuma Liverpool ta sake zira kwallo ta hudu.

Idan dai Chelsea ta doke Bayern Munich a gasar zakarun Turai a ranar 19 ga watan Mayu, to zata iya sake shiga gasar ta gaba. Domin Chelsea zata haramtawa kungiyar da tazo matsayi na hudu a Tebur shiga gasar zakarun turai.

Chelsea yanzu tana a matsayi na 6 a Teburin Premier, maki biyar tsakaninta da Tottenham da ke a matsayi na hudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.