Atletico Madrid ta lashe kofin Europa
Wallafawa ranar:
Atletico Madrid ta lashe kofin gasar Turai na Europa League karo na biyu cikin shekaru uku, bayan ta lallasa makwabciyarta Athletic Bilbao ci 3-0.
Radamel Falcao ne ya fara zira kwallaye biyu a ragar Bilbao daga bisa ni kuma Diego ya sake zira kwallo ta uku.
A kakar wasa biyu da suka gabata Atletico Madrid ta doke kungiyar Fulham ci 2-1 a wasan karshe.
Yanzu haka birnin Madrid a Spain ya sake barkewa da buki, bayan kammala bukin Real Madrid da ta lashe kofin La liga a makon jiya.
Daruruwan magoya bayan Atletico Madrid ne mata da maza da yara suka fito saman tituna domin murna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu