Boxing

Hukumar Boxing a Birtaniya ta la’anci Damben kece raini tsakanin Chisora da Haye

Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus
Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus REUTERS/Action Images/Andrew Couldridge

Hukumar Damben Boxing a kasar Birtaniya ta la’anci Damben kece raini da aka shirya gudanarwa a watan Yuli tsakanin Dereck Chisora da David Haye, tare da gargadin daukar mataki akan duk wanda ya shirya gudanar da Damben.

Talla

Tun a watan Maris ne hukumar Damben ta karbe lasisin Damben Chisora, sanadiyar wani damben bayan fage da suka yi tsakanin shi da Haye bayan a bara Chisora ya sha kashi hannun zakaran Damben na Duniya Vitali Klitschko a Munich.

Hukumar kuma tace Haye baya da izinin yin damben saboda yin ritayarsa bayan ya sha kashi hannun Wladimir Klitschko a bara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.