Premier

Manchester City ta lashe kofin Premier

Carlos Tevez yana da rike da kofin Premier tare da Roberto Mancini kocin Manchester City a lokacin da suka lashe kofin bayan doke QPR ci 3-2
Carlos Tevez yana da rike da kofin Premier tare da Roberto Mancini kocin Manchester City a lokacin da suka lashe kofin bayan doke QPR ci 3-2 REUTERS/Phil Noble

Manchester City ta karbe kofin Premier hannun Manchester United a bana bayan samun nasara a akan QPR ci 3-2 a wasannin karshe da aka gudanar na Premier. Kodayake Manchester United ta doke Sunderland ci 1-0 amma City ta lashe kofin ne da yawan kwallaye.

Talla

Wannan ne karo na farko da Manchester City ta lashe kofin premier a Ingila bayan kwashe shekaru 44 ba tare da jin kamshin kofin ba.

Saura dai kiris kofin Premier ya kubuce wa Manchester City bayan kammala mintina Cas’in na wasan ana ci 2-2 tsakaninta da QPR, sai dai cikin mintina biyar da aka kara ne Sergio Aguero ya zira kwallon karshe da yaba City nasara.

A sakon shi zuwa ga Manchester City, Sir Alex Ferguson yace City tana da sauran aiki a gabatanta kafin ta kwantanta kanta da nasarorin Manchester United.

A bana dai Manchester City ta lallasa Manchester United gida da waje domin a watan Octoba Manchester City ta lallasa United ci 6-1 a Old Trafford, wasan da Ferguson ba zai taba mantawa ba a rayuwar shi.

A ranar 30 ga watan Afrilu ne kuma City ta sake doke United ci 1-0 a filin wasa na Etihad bayan Lallasa Chelsea ci 2-1 a watan Maris.

A bana dai Manchester United ta nemi lashe kofin Premier ne karo na 20.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.