Kwallon Kafa

An kammala Seria A da Premier da La liga da Bundesliga

Wani hoton da aka hada tsakanin Messi da Ronaldo da Yaya Toure wanda kuma ke dauke da tambarin Rediyon Faransa da gidan Telebijin na France 24
Wani hoton da aka hada tsakanin Messi da Ronaldo da Yaya Toure wanda kuma ke dauke da tambarin Rediyon Faransa da gidan Telebijin na France 24

Bayan kammala Seria A da Premier da La liga da Bundesliga, mun yi nazari game da kungiyoyin da suka lashe league league da kungiyoyin da zasu haska a gasar zakarun Turai da Europa a badi da kuma kungiyoyin da ba su sha da dadi ba wadanda suka fice daga aji na farko zuwa na biyu.

Talla

Spain

A Spain, kungiyar Real Madrid ce ta lashe kofin la liga a bana, kuma ita ce kungiyar da zata jagoranci tawagar kungiyoin Spain guda uku zuwa gasar zakarun Turai, Barcelona da ta zo a matsayi na biyu a Tebur da kuma Valencia a matsayi na uku.

Kungiyar Malaga ita ce kungiyar da ta zo matsayi na Hudu a La liga amma sai ta yi fafatwar neman shiga gasar zakarun Turai da wasu kungiyoyi a kasashen Turai.

Bayan kammala La liga dan wasan Malaga Ruud Van Nistelrooy ya bayyana matakin yin bankwana da kwallon kafa.

Amma kungiyar Atletico Madrid data zo matsayi na Biyar da Lavente a matsayi na shida su ne kungiyoyin da zasu haska a gasar Turai ta Europa.

Kungiyoyin da kuma suka fice a La liga a bana su ne Villarreal da Sporting Gijon. da Racing.

Jamus

A kasar Jamus, kungiyar Borussia Dortmund ce ta lashe kofin Bundeliga, kuma da ita da Bayern Munich da ke bi mata a Tebur a matsayi na biyu da Schalka 04 a matsayi na uku zasu wakilci Jamus a gasar Zakarun Turai, sai kuma kungiyar Bayern Leverkusen da zata wakilci Jamus a gasar Turai ta Europa da kungiyar Stuttgart da Hanover amma sai sun yi fafatwar neman shigar gasar.

Ingila

A Ingila, kungiyar Manchester City ce ta lashe kofin Premier league kuma Manchester United da Arsenal ne zasu take mata baya zuwa gasar Zakarun Turai, Tottenham kuma sai ta yi fafatwar neman shiga gasar da wasu kungiyoyin Turai kafin ta samu wakilci a gasar.

Kungiyar Newcastle ce kuma zata haska a gasar Turai ta Europa League.

Amma kungiyar Bolton wonders da Blackburn da Wolves su ne suka fice Premier a bana.

Bayan da City ta lashe kofin Premier wani labari da ya ja hankali shi wani hoto da aka nuna Tevez ya daga wata takarda mai dauke da bayanin cewa Allah ya jikan Ferguson.

Yanzu haka dai Manchester City ta nemi afuwa game da laifin Tevez.

Ana dai tunanin Tevez ya aikata haka ne domin mayar da martani ga Ferguson wanda a shekarar 2009 aka tambaye shi ko Manchester City zata iya ba United kunya? nan take ne kuma Farguson ya kada baki yace ba dai a zamanin shi ba.

Italia

A kasar Itaila, kungiyar Juventus ce ta lashe kofin Seria A a bana. Sai AC Milan da ke bi mata a Tebur, kuma Jeventus da AC Milan da Udinese ne zasu wakilci Italia a gasar zakarun Turai, kodayake Udinese sai ta yi fafatwar neman shiga gasar da wasu kungiyoyin Turai.

Kungiyar Lazio da Napoli sune zasu wakilci Italia a gasar Turai ta Europa League bayan zuwansu na hudu da na biyar a Teburin Seria A.

Kungiyar Lecce da Novara da Cesena sune suka fice daga Seria A zuwa Seria B.

Holland

A kasar Hollande, kungiyar Ajax ce ta lashe kofin league din kasar sai Feyernood da ke bi mata wadanda kuma zasu wakilci Hollande zuwa gasar zkarun Turai.

PSV Eindhoven da AZ Alkmar ne zasu haska a gasar Turai ta Europa League.

Amma kungiyar VVV Venlo da Excelsior da Grafschap sune suka fice babba gasar kasar.

Faransa

A Faransa, sai a karshen mako ne za’a kammala league din kasar, amma kungiyar Montpellier ita ke neman lashe kofin French league karo na farko saboda maki uku da ke tsakaninta da PSG, kungiyar Lille da ta lashe kofin a bara ita ce a matsayi na uku sai Lyon a matsayi na hudu..

kungiyoyin da ake wa barazanar ficewa daga League a Faransa sune Ajaccio da Dijon da Auxerre.

Portugal

A kasar Potugal, kungiyar FC Porto ce ta lashe kofin Portuguese Liga sai kungiyar Benfica de ke bi mata a matsayi na biyu kuma sune kungiyoyin da zasu haska a gasar zakarun Turai amma Braga da ke a matsayi na uku a Tebur sai yi fafatawar neman shiga gasar.

Kungiyar Sporting Lisbon da Moritimo sune zasu haska a gasar Turai ta Europa League.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.