Ingila

Hodgson ya ajiye Ferdinand a tawagar Ingila zuwa gasar Turai

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand
Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand REUTERS/Nigel Roddis

sabon kocin ‘Yan wasan Ingila, Roy Hodgson ya ajiye Rio Ferdinand cikin tawagar shi da zasu haska a gasar cin kofin Turai a kasashen Ukraine da Poland. A yau laraba da misalin karfe 1 agogon GMT ake sa ran za’a bayyana sunayen ‘Yan wasan Ingila da zasu bugawa kasar wasa a gasar cin kofin Afrika da za’a fara a watan gobe.

Talla

Sai dai Jaridar The Sun a birtaniya tace Hodgson ya tabbatar mata da cewa Rio Ferdinan baya cikin tawagar shi.

Tun watan Yunin bara da Ingila ta buga wasa da Switzerland, Ferdinand bai sake bugawa Ingila wasa ba saboda rauni.

Ana dai tunanin za’a hada sunan John Terry dan wasan Chelsea cikin tawagar Ingila bayan karbe shugabancin ‘Yan wasan daga hannun shi a watan Fabrairu saboda nuna wariyar launin fata ga Anton Ferdinand.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.