Ingila

Hodgson ya hada sunan Terry a tawagar Ingila zuwa Euro

John Terry,Dan wasan kungiyar Chelsea
John Terry,Dan wasan kungiyar Chelsea REUTERS/Stefan Wermuth

John Terry yana cikin ‘Yan wasan Ingila da zasu haska a gasar cin kofin Turai, duk da dan wasan yana fuskantar shari’a akan nuna wariyar launin fata ga dan wasan QPR Anton Ferdinand.

Talla

Sanadiyar karbe jagorancin ‘Yan wasan Ingila ne daga hannun Terry ya yi sanadiyar Fabio Capello ajiye aikin horar da ‘yan wasan Ingila.

Yanzu kuma Roy Hogdson wanda ya gaji Capello ya hada sunan Terry cikin ‘yan wasan shi 23 da zasu kai ziyara Ukraine da Poland.

Hodgson yace sai an kammala shari’ar Terry ne za’a iya cewa yana da laifi.
Rio Ferdinand dai an tsame sunan shi daga cikin tawagar.

Kuma yanzu Steven Gerrard ne Hodgson ya zaba matsayin Kaftin, jagoran tawagar Ingila.

A ranar 11 ga watan Yuni ne Ingila zata buga wasan farko da Faransa, kafin ta kece raini tsakaninta da Sweden da kuma Ukraine mai masaukin baki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.