Kwallon Kafa

Liverpool ta sallami Kenny Dalglish

Kocin Liverpool Kenny Dalglish
Kocin Liverpool Kenny Dalglish REUTERS/Phil Noble/Files

Liverpool ta salami kocinta Kenny Dalglish, bayan kasancewar Liverpool matsayi na 8 a teburin Premier. Dalglish mai shekaru 61 ya taimakawa Liverpool lashe kofin Carling tare da buga wasan karshe da Chelsea a gasar FA. Amma Liverpool bata samu hurumin shiga gasar zakarun Turai ba a kakar wasa mai zuwa.

Talla

A cikin sanarwar sallamar Dalglish, Liverpool tace sakamakon Premier League abun takaici ne don haka idan za’a cim ma nasara to sai an samu sauyi.

Yanzu haka dai rehotanni na nuni da cewa kocin Wigan ne Roberto Martinez da tsohon kocin Liverpool Rafael Benitez ake ganin zasu gaji Dalglish. Ko kuma kocin Norwich Paul Lambert.

Sallamar Dalglish dai keke da keke aka yi tsakaninshi da masu Liverpool John W Henry da Tom Werner a Boston.

A watan Janairu ne Liverpool ta dauki Dalglish matsayin koci, sai dai kungiyar bata cim ma riba ba domin tazarar maki 37 ne Manchester City taba Liverpool a Teburin Premier.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.