Montpellier ko PSG: Fafatawar karshe a Faransa
Wallafawa ranar:
A karshen makon ne za’a kammala league a kasar Faransa, kuma kungiyar Montpellier ce ke shirin lashe kofin gasar karo na farko, bayan samun tazara maki uku tsakaninta da PSG.
A ranar Lahadi ne dai kungiyoyin Faransa zasu buga wasa lokaci daya, kuma Montpellier, zata kara ne da Auxerre kungiyar da zata fice gasar a bana.
Bayan kammala wasannin a karshen makon za’a tantance kungiyoyin da zasu buga gasar zakarun Turai da Europa League da kuma kungiyoyin da zasu bi sahun Auxerre a hanyar ficewa gasar.
Montpellier da PSG sun tsallake gasar zakarun Turai.
A karshen mako nan Montpellier, tana neman kunnen doki ne ta lashe kofin, PSG kuma zata yi fatar a lallasa Montpellier, tare da neman doke Lorient kafin ta lashe kofin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu