Kwallon Kafa

Zakarun Turai: Munich zata karbi bakuncin Chelsea a wasan karshe

Wani mayafi da aka daura a harabar shiga filin wasan Stamford Bridge mai dauke da bayanin wasan karshe tsakanin Bayern Munich da Chelsea.
Wani mayafi da aka daura a harabar shiga filin wasan Stamford Bridge mai dauke da bayanin wasan karshe tsakanin Bayern Munich da Chelsea. REUTERS/Eddie Keogh

Kungiyar Bayern Munich zata karbi bakuncin Chelsea a wasan karshe na gasar Zakarun Turai a gobe Assabar, inda Chelsea zata nemi lashe kofin karo na farko a cikin filin wasan Allianz Arena, bayan Manchester United ta haramtawa Chelsea kofin shekaru hudu da suka gabata da birnin Moscow a shekarar 2008.

Talla

Amma Bayern Munich tana neman lashe kofin ne karo na 5 bayan buga wasan karshe shekaru biyu da suka gabata tsakaninta da Inter Milan. Amma Inter Milan ce ta lashe kofin bayan doke Bayern ci 2-0.

A bana dai Bayern Munich ta sha kashi hannun Borussia Dortmund gida da waje, tare da haramta wa Munich kofin Bundesliga da kofin kasar Jamus.

Amma dan wasan Munich, Arjen Robben yace a gobe Assabar zasu lashe kofi mafi girma a Turai.

A daya bangaren kuma duk da cewa an kammala Premier Chelsea tana matsayi na 6 a Tebur, amma ‘Yan wasan The Blues sun lashe kofin FA bayan doke Liverpool sannan suka yi waje da Barcelona mai rike da kofin zakarun Turai.

Kodayake Bayern Munich ce ta yi waje da Real Madrid a bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagayen kusa da karshe.

Kungiyoyin biyu zasu buga wasan gobe ba tare da wasu zaratan ‘yan wasan su ba.

Akwai ‘yan wasan bayern guda uku Holger Badstuber, David Alaba and Luiz da aka haramtawa buga wasan karshe saboda karbar kati biyu a wasan da Munich ta doke Madrid.

Chelsea kuma ‘Yan wasanta hudu ne John Terry, wanda aka ba Jan kati a wasan Barcelona sai kuma Raul Meireles, da Ramires da kuma Branislav Ivanovic dab a zasu harka ba a Munich.

Hukumar EUFA dai ta tabbatar da sunan Pedro Proenca dan kasar Portugal a matsayin wanda zai yi alkalancin wasan a Allianz Arena.

A bana dai Mista Proenca ya yi alkalancin wasanni biyar a gasar zakarun Turai.
Yan wasan bayern Munich 11 da ake has ashen zasu haska a wasan sun hada da Manuel Neuer; Philipp Lahm (Jagora), Jerome Boateng, Daniel van Buyten, Rafinha, Bastian Schweinsteiger, Anatoliy Tymoshchuk; Arjen Robben, Toni Kroos, Franck Ribery, Mario Gomez. Sai Kocinsu Jupp Heynckes.

Yan wasan Chelsea 11 da zasu haska sun hada da Petr Cech, Jose Bosingwa, David Luiz, Gary Cahill, Ashley Cole; Frank Lampard (Jagora), John Obi Mikel, Salomon Kalou, Juan Mata, Daniel Sturridge, Didier Drogba. Sai kocinsu Roberto Di Matteo.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.