Kwallon Kafa

Chelsea ta lashe kofin Gasar Zakarun Turai

'Yan wasan Chelsea cikin wata Motar Bus suna zagayawa a Birnin London domin murnar lashe kofin gasar zakarun Turai
'Yan wasan Chelsea cikin wata Motar Bus suna zagayawa a Birnin London domin murnar lashe kofin gasar zakarun Turai Reuters

Dubun dubatar magoya bayan Chelsea ne suka tarbi tawagar ‘yan wasan a birnin London bayan samun nasarar lashe kofin zakarun Turai karo na farko a tarihin kungiyar. A ranar Assabar ne Chelsea ta lashe kofin zakarun turai bayan samun galabar Bayern Munich a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan kammala mintinn wasan ana ci 1-1.

Talla

Chelsea dai ta yi wa Bayern Munich haramiyar kofin ne a Munich a filin wasanta. Kuma a bana Bayern Munich ta tashi a tutar babu; babu kofin Bundesliga babu kofin Jamus babu kuma kofin Zakarun Turai.

Yanzu haka kuma Chelsea ta haramtawa kungiyar Tottenham hurumin shiga gasar zakarun Turai a kaka mai zuwa saboda lashe kofin a bana. Domin a bana an kammala Premier, Chelsea tana matsayi na 6 a teburin gasar, al’amarin da yasa dole sai Chelsea ta lashe kofin Zakarun Turai a bana kafin ta tsallake zuwa gasar a kaka mai zuwa.

A bana dai an kammala Premier Tottenham tana matsayi na Hudu a Tebur wanda zai bata damar haskawa a gasar Zakarun Turai a kaka mai zuwa. Amma yanzu bayan Chelsea ta lashe kofin Zakarun Turai dole Tottenham ta haki gaba.

Hukumar EUFA ta canza tsarinta ne a shekarar 2005, lokacin da Liverpool ta lashe kofin zakarun Turai a Istanbul kuma a shekarar amma Liverpool bata tsallake zuwa gasar ba.

A shekarar ne kuma Hukumar EUFA ta ba Liverpool damar haskawa a gasar, matakin da yaba kungiyoyin Ingila biyar damar haskawa a gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.