French League

Montpellier ta lashe kofin League a Faransa

'Yan wasan kungiyar  Montpellier, a lokacin da suke murnan lashe kofin league na Faransa
'Yan wasan kungiyar Montpellier, a lokacin da suke murnan lashe kofin league na Faransa Reuters

Kungiyar Montpellier ta lashe kofin league a Faransa karo na farko bayan lallasa kungiyar Auxerre ci 2-1 a wasannin karshe da aka gudanar a jiya Lahadi.

Talla

John Utaka na Najeriya shi ne ya zira kwallaye biyu a ragar Auxerre bayan Livier Kapo ya fara zira kwallon farko a ragar Montpellier.

An kammala French league, maki uku tsakanin Montpellier da PSG. Kuma wannan ne karo na farko da Montpellier ta lashe wani kofi tun shekarar 1990 da kungiyar ta lashe kofin gasar Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.