Kwallon Kafa

Drogba yace zai yi bankwana da Chelsea

Didier Drogba dan wasan Chelsea  rike da kofin zakarun Turai
Didier Drogba dan wasan Chelsea rike da kofin zakarun Turai REUTERS/Olivia Harris

Wata Mujallar wasanni a Faransa tace Dan kasar Cote d’Ivoire Didier Drogba ya kwarmata wa abokan wasan shi zai yi bankwana da Chelsea, saboda gajiya da zama saman Benci bayan taimakawa Chelsea lashe gasar gasar zakarun Turai karo na farko.

Talla

Drogba ne dai ya zira kwallon karshe a ragar Bayern Munich a bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda ya ba Chelsea nasarar lashe kofin zakarun Turai karo na farko a Tarihin kungiyar.

Amma mujallar France Football tace dan wasan ya barke da kuka a gaban abokan wasan shi bayan kwarmata masu zai yi bankwana da Chelsea a lokacin da ‘yan wasan ke zagayawa a cikin birnin London da kofinsu saman Mota.

A cewar Mujallar, Drogba yace zai yi bankwana da abokan wasan shi a kaka mai zuwa.

Wannan dai na zuwa ne bayan Fernando Torres yace Kakar wasan bana ce Kaka mafi muni a rayuwar shi. Hakan kuma ke nuna alamun Torres zai yi bankwana da Chelsea a kaka mai zuwa.

Torres dai yana ganin ba a yi mashi adalci ba da aka jiye shi a banci fara wasan karshe tsakanin Chelsea da Bayern Munich a gasar zakarun turai.

Yanzu haka dai Rahotanni daga ingila na cewa Torres zai gana da shugabannin Chelsea game da makomar shi

Yanzu, Torres da Yuan Mata abokin wasan shi a Chelsea, Vicente del Bosque ya hada sunan su cikin kwarya kwaryar tawagar ‘Yan wasan Spain, kwanaki uku bayan sun taimakawa Chelsea lashe gasar zakarun Turai.

A ranar 27 ga watan Mayu ne dai Vicente del Bosque zai bayyana ‘Yan wasan shi da zasu bugawa Spain wasa a gaasar Cin kofin Turai da za’a gudanar a kasashen Ukraine da Poland.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.