Tennis

Rafael Nadal ya lashe Italian Open

Rafael Nadal sanye da bakar riga rike da kofin shi tare da Novak Djokovic.
Rafael Nadal sanye da bakar riga rike da kofin shi tare da Novak Djokovic. REUTERS/Olivier Anrigo

Rafael nadal ya lashe kofin Italian Open bayan ya doke Novak Djokovic a wasan karshe, kuma wannan ne kofin Italia na shida da dan wasan ya lashe. A ranar Lahadi ne dai aka shirya gudanar da wasan, amma saboda ruwan sama da aka tabka a birnin Rome aka dage wasan zuwa ranar Litinin litinin.

Talla

Wannan nasarar Yanzu yasa Nadal ya dawo shi ne na biyu a duniya a fagen Tennis.

Tun bayan wasan karshe a Monte Carlo Masters a bara, Sau bakwai a jere ne dai Djokovic ke samun galabar Nadal.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.