Wasanni

FIFA bata son bugun daga-kai-sai-mai-tsaron gida

Shugaban Hukumar FIFA  Sepp Blatter
Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Sepp Blatter ya ce irin bugun daga kai sai mai tsaron gida, wato penalies kicks, da ake buga wa don fidda wanda ya yi nasara a wasa, balai ne da ke fidda armashin wasan kwallo. Blatter ya yi wannan jawabin ne a gaban wakilan hukumar da ke taron su.Yace bai kamata wasan kwallon kafa ya zama na mutane 2 ba kawai, wato mai buga kwallon da mai tsaron gida.A baya bayan nan, sai da aka yi irin wannan bugun kafin a fidda wadanda suka yi nasara a manyan wasanni 2, wato gasar Champions League, inda Chelsea fa fidda Bayern Munich da ci 4 da 3 a irin wanna bugun na Penalty, sannan kuma a gasar cin kofin nahiyar Africa wato African Cup of Nations, Zambia ta fidda Ivory Coast ci 8 da 7 a irin wannan hali.Don haka ne Blatter ya kalubalanci wani kwamiti hukumar karkashin Franz Beckenbauer da ya samar da mafita kan wannan.