Kwallon Kafa

Guardiola zai yi fatar lashe kofin karshe a Copa del Ray

Josep Guardiola Kocin  FC Barcelona wanda zai yi bankwana da Kungiyar a Yau Juma'a a wasan karshe da Athletic Bilbao a Copa del Ray.
Josep Guardiola Kocin FC Barcelona wanda zai yi bankwana da Kungiyar a Yau Juma'a a wasan karshe da Athletic Bilbao a Copa del Ray. REUTERS/Sergio Carmona/Files

A yau u Juma’a ne ranar karshe da Pep Guardiola zai jagoranci ‘yan wasan Barcelona a matsayin kocin kungiyar, a wasan karshe na Copa Del ray da Barcelona zata fafata da Athletic Bilbao.

Talla

Akwai yiyuwar dai Guardiola zai sake lashe wani kofi kafin ya yi bankwana da Barcelona. Kuma Kofin Copa Del ray shi ne kofin da Gurdiola bai lashe sau biyu ba a shekarun daya kwashe a Barcelona.

Domin ya lashe kofin La liga sau uku, da kofin zakarun Turai sau Biyu da kofin Duniya na kungiyoyin kwallon kafa sau biyu da Super Cup na Turai guda biyu da Super Cup uku a Spain.

Andres Iniesta da Fabregas sun ce a yau zasu lashe kofin da zasu saudakar da shi ga Guardiola.

Sai dai Athletic Bilbao ba kwanwar lasa bace domin zata nemi lashe kofin ne domin huce hushin kofin Europa League da Atletico Madrid ta haramta wa Bilbao.

Kodayake tun fara aikin Guardiola matsayin kocin Barcelona, kungiyar Bilbao bata samu galabar shi ba don ya lallasa ta sau 9 a wasanni 14, kuma sauran wasannin Biyar, duka kunnen doki aka yi.

A bana dai babu wani kofi da Barcelona ta lashe domin Real Madrid ta karbe kofin La liga hannunta, kuma Chelsea ce ta yi waje da Barcelona a gasar zakarun Turai.

Don haka Kofin Copa del Ray shi ne kofin da yanzu Barcelona ta sa wa ranta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.