Kwallon Kafa

Liverpool na gab da daukar Martinez matsayin Koci

Roberto Martinez Kocin kungiyar Wigan wanda Liverpool ke neman dauka sabon koci bayan Sallamar Dalglish
Roberto Martinez Kocin kungiyar Wigan wanda Liverpool ke neman dauka sabon koci bayan Sallamar Dalglish Reuters

Dave Whelan Shugaban kungiyar Wigan, yace Roberto Martinez yana gab da kulla yarjejeniya da Liverpool domin zasu gana a Miami. Tuni Wigan taba Liverpool damar tattaunawa da Martinez kuma Whelan shugaban Wigan yaba kocin wa’adi daga nan zuwa 5 ga watan Yuni domin yanke hukunci akan makomar shi.

Talla

Bayan kammala wasannin Premier a bana ne dai Liverpool ta kori Kenny Dalglish daga Anfield Saboda rashin gamsuwa da sakamakon Premier a bana.

Robeto Mertinez a bana ya taka rawar gani domin ya taimaka wa Wigan ci gaba da zama a Premier, bayan ya doke Liverpool da Arsenal da Manchester United da Newcastle.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.