Wasanni

Spain bata son ana mata kallon gwana

Alamar gasar cin kofin nahiyar Turai EURO 2012
Alamar gasar cin kofin nahiyar Turai EURO 2012 DR

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafan kasar Spain, wadda ita ce ke rike da kofin kwallon kafa na nahiyar turai, da ma kofin duniya, yace ‘yan wasan nasu ba su son a rinka zuga su ana cewa su ne za su yi rawar gani a gasar cin kofin turai wato Euro 2012. Dan wasan mai suna Sergio Ramos ya ce suna sane da cewa ana musu kallon gwanaye, amma ba su so su zauna kan abin da ya riga ya wuce, don haka dole a kowace rana suke  ji kamar yau suka fara fita atisaye.A rukunin su na 3, ranar 10 ga watan Yuni spain za ta buga wasan ta na farko a gasar  EURO 2012, inda za ta kara da Italy, da it ace zakarar duniya ta shekarar 2006, daga baya kuma za su buga wasa da Ireland da kuma Croatia.