Wasanni

Sudan ta kudu ta sami shiga FIFA

Alamar hukumar FIFA
Alamar hukumar FIFA

kasar sudan ta kudu ta zama member hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, inda ta zama ta 209, a jerin kasashen da ke da wakilci a hukumar. Yanzu kasar ta Sudan ta kudu ba ta kai shekara 1 da samun yancin kanta daga sudan ba.Kashi 98 cikin 100 na wakilan hukumar ta FIFA ne suka kada kuri’ar amicewa da shigar sudan din.Shugaban hukumar kwallon kafan sudan ta kudu, Oliver Mori Benjamin, yace har yanzu kasar na cikin halin yaki, amma za su bunkasa kwallon kafa don kawar da yaki da yake yake da yunwa.