Spain ta doke Serbia amma Jamus da Holland sun sha kashi
Wallafawa ranar:
Kasar Spain mai rike da kofin Turai ta nuna a shirye take domin ta lallasa kasar Serbia ci 2-1 a wasannin sada zumunci da kasashe suka gudanar a karshen mako, makwanni biyu masu zuwa a fara fafata gasar cin kofin Turai.
Sai dai Holland da Jamus basu sha da dadi ba, domin Jamus tasha kashi hannnun Switzerland ci 5-3. Bulgaria kuma ta doke Holland ci 2-1.
Jamus da Hollande dai a rukuni daya aka hada su a gasar Turai, Tare da Portugal da Denmark.
Sai dai wasa tsakanin Portugal da Macedonia an tashi ne babu ci 0-0. Brazil kuma ta lallasa Denmark ci 3-1.
Faransa dai tasha da kyar ne hannun Iceland domin an tashi wasan ne ci 3-2.
Tun da farkon fara wasan ne dai Iceland ta zira kwallaye biyu a ragar Faransa kafin daga bisani Faransa ta barke kwallaye tare da sake zira kwallo ta uku.
Ingila kuma ta samu galabar Norway ci 1-0 kuma wannan ita ce nasara ta farko Roy Hudgson ya samu a fara aikin horar da ‘yan wasan Ingila.
Wasannin sada zumunci da aka gudanar dai wata dama ce ga kasashen domin tantance ‘yan wasan da suka dace su haska a gasar cin kofin Turai da za’a gudanar a kasashen Polande da Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu