Tennis

Nadal da Djokovic da Federer sun haska a French Open

Dan kasar Argentina  Juan Martín Del Potro,  a lokacin da yake fafatawa a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa
Dan kasar Argentina Juan Martín Del Potro, a lokacin da yake fafatawa a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa

Rafeal Nadal wanda ya lashe kofin Roland Garros sau shida, a yau Talata ne zai kara da Simone Bolelli na Italia a zagaye na uku. Nadal yana neman lashe kofin French Open ne na bakwai bayan ya lashe kofin a shekarar 2005 da 2006 da 2007 da 2008 da 2010 da kuma bara 2011.

Talla

A haskawar shi ta farko, Novak Djokovic ya samu nasarar tsallakewa zuwa zagaye na biyu. Haka ma Roger Federer ya tsallake zuwa zagaye na biyu.

A bangaren mata kuma a yau ne Maria Sharapova ta Rasha zata kara da Alexendra ta Romania, sai Serena Williams ta Amurka zata kece raini da Virginia ta Faransa.

A jiya Litinin, Victoria Azarenka tasha da kyar ne a fafafatwar farko amma a yau zata kara ne da Dinah ‘yar kasar Jamus.

A jiya ne Li na ‘Yar kasar China mai rike da kofin Roland Garros ta samu nasarar doke Sorana ta Romania.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.