Kwallon Kafa

Balotelli yace zai kashe duk wanda ya jefa masa Ayaba a Euro

Dan wasan Itaila Mario Balotelli
Dan wasan Itaila Mario Balotelli Reuters

Mario Balotelli dan wasan Italiya yace zai dauki matakin yin kisa ga duk wanda ya jefa ma shi Ayaba a filin wasa ko saman titi a lokacin wasannin gasar cin kofin Turai da za’a gudanar a kasashen Ukraine da Poland.

Talla

Mario Balotelli dai yasha fama da matsalar nuna masa wariyar launin fata musamman lokacin da yake taka kwallo a Italiya. Kuma akwai yiyuwar bakaken fata zasu yi fama da matsalar wariyar launin fata a gasar cin kofin Turai.

Balotelli a lokacin da yake zantawa da wata mujallar wasanni a Faransa, dan wasan yace sai dai da daure shi a gidan yari amma sai ya kashe duk wanda ya jefa masa bawan Ayaba.

A Turai dai a filin wasa ‘yan kallo sukan jefa wa bakaken fata bawan Ayaba da nufin danganta su da Birai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.